Luke 17

Zunubi, Bangaskiya da Aiki

1Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwa da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa. 2Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi. 3Saboda haka, ku lura da kanku.

“In ɗanʼuwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.
4In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”

5Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”

6Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.

7“In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba?’ 8Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba?’ 9Shin, zai gode wa bawan don ya yi aikin da aka ce ya yi ne? 10Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”

An Warkar da Kutare Goma.

11Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”

14Da ya gan su sai, ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtace.

15Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.

17Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtace ba? Ina sauran taran? 18Ba wanda ya dawo don ya yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” 19Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai. ”

Zuwan Mulkin Allah

20Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin ƙallon ku ba. 21Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”

22Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin bin su. 24Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. 25Amma da fari, dole ya sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.

26“Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. 27Mutane suna ci, suna sha, suna auraya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Saʼan nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.

28“Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. 29Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. 31A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don ya kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada ya koma don wani abu. 32Ku tuna fa da matar Lot! 33Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. 34Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 35Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 36(Maza biyu za su kasance a gona, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan).”

37Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”

Copyright information for HauSRK